28 Yuli 2026 - 23:06
Source: ABNA24
FT: Iran Ta Ƙara Dagula Ma'aunin Amurka Da Isra'ila Ta Hanyar Sake Gina Ƙarfin Makamanta Masu Linzami

Jaridar Ingila Financial Times, a cikin wani rahoto tana mai nuni ga ayyukan Iran a 'yan watannin da suka gabata, ta rubuta cewa, Jamhuriyar Musulunci, duk da hare-hare masu yawa, ta sami nasarar kiyaye ƙarfin makamanta masu linzami, kuma ta hanyar sake gina ƙarfin sojinta cikin sauri, ta ƙara dagula ma'aunin Amurka da gwamnatin yahudawa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A cewar Financial Times, Iran, ko da bayan hare-hare masu tsanani, ta ci gaba da aiwatar da hare-haren makamai masu linzami masu daidaito d nagarta a kan manufa daban-daban, kuma ta nuna cewa ta kiyaye ƙarfin makamanta masu linzami. Financial Times ta yi iƙirarin cewa, waɗannan hare-haren sun kai hari a kan wasu sansanoni da cibiyoyin sojin Amurka da kawayenta a yankin.

Wannan rahoto, tare da dogaro da ra'ayin ƙwararrun soji na yamma, ya kara da cewa, Tehran ta koyi darasi daga hare-haren da suka gabata, kuma ta dogara da ababen more rayuwa na ƙarƙashin ƙasa da ƙarfin cikin gida, ta sami nasarar sake gina da sabunta wani muhimmin sashe na ƙarfin makamanta masu linzami.

"Nicole Grajewski," mai bincike kan shirin makamai masu linzami na ballastic na Iran a Cibiyar Harkokin Duniya ta Faransa, a cikin hira da wannan jarida, ta jaddada cewa, injiniyoyin Iran sun sami nasarar kiyaye ƙarfin kera da sake gina tsarin makamai masu linzami, kuma sun yi amfani da cibiyoyin ƙarƙashin ƙasa don ci gaba da wannan tsari.

Financial Times ta kuma yi nuni ga damuwar jami'an Amurka game da raguwar yawan makamai masu linzami masu kakkabo makamai, kuma ta rubuta cewa, yawaitar amfani da waɗannan tsarin a 'yan watannin da suka gabata, ya sanya ƙarfin tsaron Amurka da kawayenta cikin matsin lamba, kuma wannan batu zai taka muhimmiyar rawa a shawarar Washington na gaba.

A ci gaban rahoton yazo, Iran sannu a hankali tana amfani da makamai masu linzami na zamani da daidaito; lamarin da ya sa kama su ya fi wahala. A rubutun wannan jarida, makamai masu linzami kamar "Khaibar Shikan," saboda ƙarfin motsi a matakin ƙarshe na tafiya, suna haifar da ƙalubale mai tsanani ga tsarin tsaro.

Wannan jarida a ƙarshe ta kammala da cewa, duk da hare-haren da aka yi, ƙarfin makamai masu linzami na Iran bai ɓace da raguwa ba, kuma har yanzu yana da muhimmanci a matsayin abin fifikon yaƙi; lamarin da, a ganin masana, ya sanya shirin soji na Amurka da gwamnatin yahudawa cikin ƙarin sarkakiya.

………………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha